An bada shawar a daure Oscar Pistorius tsawon shekaru 10 | Labarai | DW | 17.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bada shawar a daure Oscar Pistorius tsawon shekaru 10

Rashin hukunci mai tsauri bayan kisan budurwarsa Reeva Steenkamp na iya zama wani abu da masu sanya idanu a shari'ar basu tsammata ba.

An bayyana cewa dan wasannan nakasassun dan kasar Afrika ta Kudu Oscar Pistorius, kamata ya yi ya share akalla shekaru 10 a gidan kaso, bayan kisan budurwarsa tasa a a cewar alkali mai shigar da kara, bayan da kotu ta rufe zaman sauraren wannan kara a yau Juma'a .

Mai shari'a Thokozile Masipa ta dage zaman sauraren wannan kara, har sai ranar Talata mai zuwa, inda za ta yanke hukuncin da zai kawo karshen kwashe tsawon watanni shida ana zama, a dage wannan shari'a da ta ja hankulan miliyoyin mutane a duniya.

Dan wasan nakasassun mai shekaru 27 da aka yankewa kafafu tun yana karamin yaro, an same shi da laifin kisan budurwar tashi mai shekaru 29 da ta kammala karatun lauya, kuma ta kasance mai shiga gasar kawa na masu kalula.