1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ayyana dokar ta baci kan annobar Ebola

Ramatu Garba Baba
July 18, 2019

Hukumar lafiya ta Duniya ta ayyana dokar ta baci a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango don shawo kan annobar cutar Ebola da ke kara yaduwa a kasar

https://p.dw.com/p/3MGLn
Kongo Ebola Ausbruch
Hoto: Reuters/O. Acland

Hukumar Lafiya ta WHO ta dauki matakin ne ganin girmar matsalar da kuma barazanar da yankin gabashin kasar ya fada ciki na fuskantar yaduwar cutar. Shekara guda kenan ake ta yakar cutar ba tare da an yi nasarar dakileta ba. A makon da ya gabata ma cutar ta kashe wani Fasto a yankin Goma da ke kasar ta Kwango.

Shugaban Hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce bayan dogon nazari ne suka yanke shawarar ayyana dokar. Wannan shi ne karo na hudu a tarihi da Hukumar Lafiya ta Duniya ke ayyana dokar ta baci a sanadiyar annoba mai hadari ga rayuwar dan adam.

Tun bayan bullar Ebola a watan Augustan bara a Kwangon cutar ta halaka mutum sama da 1600 daga cikin mutane 2500 da ta kama.