An amince da zuba jari don bunkasa Masar | Labarai | DW | 14.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An amince da zuba jari don bunkasa Masar

Masar ta sanya hannu kan wasu jerin yarjeniyoyi da kamfanoni da wasu kasashen na yankin gabas ta tsakiya a wani mataki na tada komadar tattalin arzikinta.

Kasashen da kamfanonin dai sun amince su sanya dubban miliyoyin daloli a fannonin da suka hada da albarkatun man fetur da makamshi da gine-gine ciki kuwa har da samar da wata sabuwar hedikwata ta kasar.

Kamfanin Jamus din nan wato Siemens ya amince da zuba jari na dala miliyan dubu goma don bunkasa samar da makamashi wanda kasar ta ce zai taimaka mata wajen cigaba cikin hanzari.

Yarjejeniyar tsakanin Masar da kasashen da ke halartar taron wanda zai kammala a gobe Lahadi ta kuma tanadi samar da abubuwa na more rayuwa da kuma habaka harkoki na kasuwanci.