An amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 10.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan ta Kudu

Bangarorin da ke rikici a kasar Sudan ta Kudu sun saka hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta domin kawo karshen rikicin da ke faruwa a kasar.

Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir da madugun 'yan tawaye Riek Machar sun saka hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta, cikin wani matakin martani daga matsin lambar kasashen duniya.

A wannan Jumma'a da ta gabata aka amince da yarjejeniyar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha. Wannan ya zama karo na farko da shugabannin suka fuskanci juna tun bayan barkewar rikici a watan Disamban 2013 kan gwagwarmayar samun madafun iko. Kiir da Machar sun amince da gwamnatin wucin gadi zuwa lokacin zaben shekara mai zuwa.

Bisa yarjejeniyar za a tsagaita wuta cikin sa'o'i 24.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal