1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amincewa da masu shiga takara a Burkina

Abdoulaye Mamane Amadou
October 8, 2020

Hukumar zaben Burkina Faso ta amince da takardun mutane 14 daga cikin 23 da ke son tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shugaban kasar da ke tafe.

https://p.dw.com/p/3jbS7
Burkina Faso Präsident Roch Marc Christian Kabore
Shugaban Burkina Faso zai sake tsayawa takaraHoto: Reuters/A. Sotunde

Daga cikin 'yan takarar da hukumar ta sahalewa tsayawa, har da shugaban kasar mai ci yanzu da ke neman zarcewa akan wa'adin mulki Roch Marc Christian Kaboré da madugun 'yan adawar kasar Zephirin Diabré hakan da wani dadden na hannun damar hambarararen shugaban kasar Blaise Compaoré wato Eddie Komboïgoda kuma firaministan gwamnatin wucin gadi ta mulkin soja da yanzu hakan ke hijira a Canada Yacouba Isaac Zida.

Sai dai hukumar zaben kasar ta ce duk da amincewar da ta yi da 'yan takarar babbar kotun tsarin mulkin kasar ce ke da cikakken hurumi na tantancewa, kana kuma tana da wa'adin kwanaki 10 nan da gaba domin aiwatar da nata bincike. A ranar 22 ga watan Nuwamban wannans hekarar ne za a gudanar da zaben shugaban kasar.