An amince da shirin kwance damara a Kodivuwa | Labarai | DW | 08.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An amince da shirin kwance damara a Kodivuwa

Manyan shugabannin Ivory Coast ko Kodivuwa su biyar da da basa ga maciji da juna sun maido da shirin wanzar da zaman lafiyar kasar bisa turba bayan sun amince su kaddamar da wani shirin kwance damara tare da kidayar jama´a wanda zai share fagen gudanar da zabe a karshen watan oktoba. A lokacin da yake magana bayan tattaunawar da suka yi a birnin Abidjan shugaban kungiyar tarayyar Afirka Denis Sassou Nguesso ya ce sun bar zauren taron bayan sun ga alamar cewa abubuwa na tafiya kamar yadda ake so. Taron dai ya samu halarcin shugaba Laurent Gbagabo da FM Charles Konan Banny da shugaban ´yan tawaye Guillaume Soro da Henry Konan Bedie na jam´iyar PDCI da kuma Alassane Watara na jam´iyar RDR.