1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An amince da karin albashi a Afirka ta Kudu

November 26, 2018

Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar Afirka ta Kudu, ya sanya hannu kan dokar karin albashi, a wani kokarin da gwamnati ke yi na kyauta jin dadin ma'aikata a kasar. 

https://p.dw.com/p/38v3g
Südafrika - neuer Präsident Cyril Ramaphosa
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Yanzu dai karancin albashi a Afirka ta Kudun, na matsayin dala daya da senti 45 a kowace sa'a guda, kwatankwacin rand dubu 3,500 wato kudin kasar a wata guda.

Dokar dai za ta fara aiki ne nan gaba, bayan gwamnatin Shugaba Ramaphosa ta kammala dukkanin abubuwan da take ganin su ne wajibai.

Masu goyon bayan karin sun ce hakan ya kawo karshen bambancin albashi da ake samu tsakanin ma'aikata a matakan kasar daban-daban.

Sai dai su kuwa wadanda ke suka, cewa suke karin zai haddasa karuwar rashin ayyukan yi, saboda ba dukkannin ma'aikatu bane za su iya biyan sabon albashin.