An ƙone wasu mutane guda bakwai a Tanzaniya | Labarai | DW | 10.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ƙone wasu mutane guda bakwai a Tanzaniya

An ƙone mutanen ne a yammacin ƙasar saboda zargin aikta laifuka na maita.

'Yan sanda a ƙasar Tanzaniya sun ba da sanarwar cewar wani gungu na jama'a cikin fushi a yammancin ƙasar.Ya ƙone wasu mutane guda bakwai ƙurmus da ransu har lahira, saboda zargin cewar sun aikata laifuka na maita.

Babban sefeto janar na 'yan sanda na yankin Jafari Mohammed ya ce sun kame mutane guda 23 waɗanda ake tuhuma da hannu a cikin kisan,kuma ya ce za a gurfanar da su a yau a gaban kotu. Lamarin dai ya faru ne a farkon wannan mako a garin Murufiti da ke a yamancin birnin Dar-Salam babban birnin Tanzaniyar.