1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Amurka za ta inganta Intanet a Afirka

May 25, 2024

Amurka ta sanar da wani shiri na inganta karfin Intanet a nahiyar Afirka zuwa kashi 80% nan da shekarar 2030, daga karfin kaso 40 da ake da shi yanzu a nahiyar.

https://p.dw.com/p/4gH8I
Hoto: Issouf Sanogo/AFP

Sanarwar da mataimakiyar shugaban kasar Amurkar Kamala Harris ta yi, ya zo ne shekara guda da ziyarar da kai nahiyar Afirka, a kuma lokacin da suka zanta da shugaban kasar Kenya William Ruto a birnin Washington.

Wannan na daga cikin manufofin Amurkar na karfafa huldar tattalin arziki da nahiyar Afirka, nahiyar da hankali ya karkata kanta a matsayin wacce makomar ci gaba na duniya ya dogara da ita.

Bankin bunkasa kasashen Afirka da ma wasu kungiyoyi sun kara himma wajen inganta fannin sadarwar zamani, inda za a fara da samar da Intanet mai karfi ga manoma a kasashen Kenya da Tanzaniya da ma Najeriya a tashin farko kafin abin ya kai ga sauran kasashe na nahiyar.