1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Amurka za ta bai wa Bangladesh tallafin Dala miliyan 202

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 15, 2024

Tallafin farko da gwamnatin rikon kwarya ta Muhammad Yunus ta samu, bayan murabus din tsohuwar firaministar kasar Sheikh Hasina

https://p.dw.com/p/4kdzz
Hoto: Sazzad Hossain/DW

Amurka ta alkawarta bai wa Bangladesh tallafin dala miliyan 202, domin ta bunkasa tattalin arzikinta da ya durkushe.

Wanna kari ne a kan dala miliyan 425 da ta ba ta baya, daga cikin dala miliyan 954 da tsara ba ta tun a shekarar 2021.

Wata tawagar mukarraban gwamnatin Amurka ce ta tabbatar da wannan alkawari, lokacin da ta ke ziyara a Dhaka babban birnin Bangladesh a Lahadin nan.

Karin bayani:Sabuwar gwamnatin riko a Bangladesh ta sha alwashin maido da dimukuradiyya

Ziyarar dai na zaman irinta ta farko tun bayan da gwamnatin rikon kwarya ta Muhammad Yunus ta kama aiki, bayan murabus din tsohuwar firaministar kasar Sheikh Hasina.

Karin bayani:Bangladesh: Firaminista Hasina ta yi murabus

Haka zalika Amurka ta kuduri aniyar tallafa wa kasar a yaki da matsalolin sauyin yanayi, tare da farfado da hanyoyin magance tauye hakkin 'dan Adam da Bangladesh ke fuskanta.