Gwamnatin Bangladesh ta sha alwashin maido da dimukuradiyya
August 9, 2024Talla
Kwana guda bayan dawowarsa gida daga Turai, Yunus ya kuma sha alwashin tabbatar da goyon baya da kuma kare kundin tsarin mulkin kasar. Mai shekaru 84 a duniya, Yunus ya kama madafan iko da kalubalen maido da kasar bisa tafarkin dimokuradiyya.
Hasina, mai shekaru 76, da ake zargi da cin zarafin bil adama da suka hada da daure abokan hamayyarta na siyasa, ta tsere da jirgi mai kirar saukar ungulu zuwa makwabciyar kasa Indiya a ranar Litinin, a yayin da masu zanga-zangar suka mamaye titunan Dhaka, babban birnin Bangladesh a karshen mulkinta na shekaru 15.