Amurka za ta aike da wasu dakaru na musamman Iraki
December 1, 2015Talla
Sakataren harkokin tsaron Amurkan Ashton Carter a yayin da yake magana a gaban kwamitin ayyukan soji yayi nuni da cewar.
Ta kara dorawa kan yakar kungiyar zamu aike da wasu dakaru a bisa umarnin shugaba Obama don murkushe ayyukan Is a Iraki,wadan nan dakurin na musamman nada ikon kwace yankunan da kungiyar ta kwace.
kalaman sakataren tsaron Amirkan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da 'yan majalisar Britaniya suke shirye-shiryen tafka muhawara ne akan ko shin sojojin kasar zasu taka rawa kan yakar Is a Syriya ne ko a'a.