Amurka ta harbo jiragen Iran marasa matuka a mashigin Hormuz
June 13, 2026
Wannan matakin na zuwa ne sa'o'i bayan da bangarorin biyu suka ce ana dab da cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin Gabas ta Tsakiya.
A jiya Juma'a ne firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya ce Amurka da Iran sun amince da kalaman da aka zayyana a yarjejeniyar sulhu da za ta kawo karshen yakin da aka fara a karshen watan Fabrairu.
Pakistan dai ta kasance mai shiga tsakani a tattaunawar da mika bayanai da kuma shawarwarin da aka cimma tsakanin bangarorin biyu a baya bayan nan.
Sharif ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X a ranar Juma'a cewa ba a taba samun lokacin da aka kai ga wannan gabar da ake kai a yanzu ba.
Bayanai daga bangarorin biyu da ke fada da juna sun nuna an sami gagarumin ci gaba.
Karin Bayani: Amurka ta yi ikrarin yin sulhu da Iran