Amurka da Koriya ta Kudu son soma atisaye | Labarai | DW | 21.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka da Koriya ta Kudu son soma atisaye

A wannan Litinin kasashen Koriya ta Kudu da Amirka suka kaddamar da wani atisayen sojoji na hadin gwiwa da zai dauki makonni biyu.

A wannan Litinin kasashen Koriya ta Kudu da Amirka suka kaddamar da wani atisayen sojoji na hadin gwiwa da zai dauki makonni biyu. Sojojin Koriya ta Kudu kimanin dubu 50 da na Amirka dubu 18 ne ke halartar wannan atisaye. Shekaru da dama kenan da kasashen biyu ke gudanar da wannan atisayen sojoji na hadin gwiwa.

Atisayen na bana na zuwa ne a daidai lokacin da barazanar yaki ta yi kamari a tsakanin Washington da Pyongyang bayan da Koriya ta Arewa ta ci gaba da yin gwajin makamai masu linzami, Koriya ta Arewa ta yi kashedi ga kasashen biyu a game da wannan atisaye da ta bayyana cewa zai kara rura wutar rikici a yankin.