1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biden da Trump sun sami tikitin yi wa jam'iyyunsu takara

Binta Aliyu Zurmi
March 13, 2024

Shugaba Joe Biden na Amurka ya sami tikitin yi wa jam'iyyarsa ta Democrats takarar shugabancin kasar a zaben watan Nuwanban shekarar nan.

https://p.dw.com/p/4dSLD
Wahlkampf in den USA - Biden vs Trump: Alte Gegner, neues Duell
Hoto: Alex Brandon/Andrew Harnik/AP/dpa

Biden wanda yanzu haka zai sake karawa da tsohon shugaban kasar Donald Trump wanda shi ma ya sami kuri'un delegets da ake bukata.

Sake tsayawa takara da shugabannin biyu za su yi, matakin da ya kai Biden da Trump kafa tarihi na kusan shekaruu 70 da ba a ga irinsa ba.

Shugaba Biden ya sami kuri'un yan jam'iyyarsa 1,968 yayin da abokin hamayarsa Donald Trump ya sami 1,215.

A Amurka dai, a hukumance dan takarar shugabancin kasa ko a jam'iyyar Republican ko ta Democrats ba ya zama cikkaken dan takara sai ya sami mafi akasarin kuri'un wakilan jam'iyyarsa da ake kira delegets.

A watan Nuwamban shekarar nan ne al'umma a Amurka kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya za su zabi sabon shugaban kasa.