1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Amurka ba za ta yi watsi da Ukraine ba

October 1, 2023

Shugaba Joe Biden na Amurka ya yi alkawarin cewa Washington ba za ta yi watsi da Ukraine da yaki ya daidaita ba, tare kuma da bukatar 'yan Republicain da su daina wasa da batun ci gaba da tallafa wa Kiev.

https://p.dw.com/p/4X1e5
Amurka ta yi alkawarin ba za ta yi watsi ba da UkraineHoto: Evan Vucci/AP/picture alliance

A cikin wani jawabi da ya yi ta kafar talabijin shugaba Joe Biden  ya jaddada wa abokan adawarsu da al'ummar Amurka cewa al'ummar Ukraine za ta ci gaba da samun goyon bayan Washington. Sannan kuma ya ce ba za su yi watsi da Ukraine ba a cikin mumunan hali da take ciki.

Karin bayani: Amurka da Ukraine na son a yi taron dangi kan Rasha

Wannan furuci na Biden na zuwa ne kwana guda bayan da 'yan majalisar dokokin Amurka suka kada kuri'a domin amincewa ko kin amincewa da tsawaita tallafin da ta ke bai wa Ukraine, inda 'yan majalisar suka dauki matakin tsuke bakin aljihu. 

Shugaban Biden ya kuma sha alwashin samar da sabon tsari na ci gaba da samar da kudade ga Ukraine a cikin kwanaki da kuma makonni masu masu zuwa duk da sabanin ra'ayi tsakaninsa da 'yan jam'iyyar Republican.

Karin bayani: Amurka za ta bai wa Ukraine sabon tallafi