Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Shirin ya kawo muku tarihin garin nan na Nguru da ke jihar Yobe a yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya da kuma tarihin fitaccen mawaki Shattima Mansur.
Wace rawa masarautun gargajiya ke takawa wajen kare tarihin al'uma daga barazanar bacewa saboda zuwar zamani da ke sanya tarihin ke neman bacewa? Alhaji Usman Dalhatu, masanin tarihin al'adun Zazzau ya bayar da amsa.
A Jamhuriyar Nijar hukumar hadin gwiwar kasashen Nijar da Najeriya ta joint Commission, ta bayyana shirye-shiryenta na saukaka harkokin zirga-zirgar jama’a da dukiyoyinsu da ma kyautata matakan tsaro.