Amnesty na fargabar gina sansanin soji a Rakhine | Labarai | DW | 12.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amnesty na fargabar gina sansanin soji a Rakhine

Gwamnatin Myanmar na gina katafaren sansanin sojoji a yankunan Musulman Rohingya da aka rugurguza yayin da rikicin kabilanci da ya dai dai ta su a baya.

A wani sabon rahoto da kungiyra kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa Amnesty International ta wallafa, ta ce akwai hotunan tauraron dan adam da ya nuna manyan tankoki na ci gaba da rusa sauran gidajen jama'a da ya rage a jihar Rakhine.

Sai dai kungiyar kare hakkin 'yan adam ta bayyan fargabar yunkurin gwamnati na samar da cibiyoyin tsaro a filayen jama'an, zai tozarta al'umman Rohingya marasa rinjye da ke sha'awar komawa gidajensu daga gudun hijira a kasar Bangaledesh.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa akalla Musulman Rohingya dubu 700,000 ne rikici ya tilastamusu tserewa matsugunansu bayan da aka zargin sojojin gwamnatin Mayanmar da kaddamar da hari a kansu cikin watan Agustan shekarar 2017.