Amnesty International ta zargi sojojin Burundi | Labarai | DW | 22.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amnesty International ta zargi sojojin Burundi

A wani rahoto da ta fitar a wannan Talatan kungiyar mai fafutukar kare hakin dan Adam ta duniya ta ce sojojin kasar Burundi sun yi kisan gilla ga jama'a.

Kungiyar kare hakin dan Adam ta Amnesty International ta zargi sojojin kasar Burundi da laifin kisan gilla ga jama'a yayin wani tashin hankali da ya barke a ranar 11 ga watan Disamba a Bujumbura babban birnin kasar, wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 87. Cikin wani rahoto da ta fitar, kungiyar mai fafutukar kare hakin dan Adam ta ce mafi yawan mutanen da aka kashe, an kashe su ne ta hanyar harbin su ga kai, kuma an ga gawawakin su suna daddaure.

Shaidun gani da ido sun bayyana yadda aka fitar da mutane da dama daga gidajansu sannan aka harbesu kai tsaye da bindiga. Kasar ta Burundi dai ta shiga cikin wani hali na tsaka mai wuya, tun bayan da shugaban kasar ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a kasar a wani haramtaccen wa'adi na uku.