Amnesty International: Sojojin Najeriya sun yi ta'asa a kan 'yan Shi'a | Siyasa | DW | 22.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Amnesty International: Sojojin Najeriya sun yi ta'asa a kan 'yan Shi'a

A rahoton da Ƙungiyar Amnesty International ta fitar ta ce ta bankado rufa –rufar da sojojin Najeriya suka yi a kan mutanen da suka kashe a hargistin da ya faru tsakaninsu da ‘yan Shi’a a Zariya.

Wannan dai shi ne kamalallem rahoto da Ƙungiyar Amnesty International ta fitar da t a ce ta bankaɗo abubuwa na asha da suka faru a arangamar da aka yi tsakanin sojojin da ‘yan Shi'a a ranar 12 zuwa 14 ga watan Disambar bara a Zaria. Amnesty ta ce binciken da ta yi da shaidu na gani da ido sun tabbatar da cewar an kashe tare da bizne fiye da mutane 350 a manyan kabarurruka ba tare da sanin ‘yan uwansu ba.

Shaidun sun tabbatar da aikata ta'asa da sojojin suka yi a kan 'yan Shi'a

Amnesty ta ce a yanzu ne fa aka fara gano abubuwa na asha na take hakin jama'a da cin zarafinsu da karkashesu da aka yi a wannan arangamar da it ace irinta ta farko da ta yi muni tsakanin sojoji da ‘yan Shi'a. Ambasada Muhammad Kawu Ibrahim shi ne daraktan Ƙungiyar Amnesty a Najeriya.

‘' Mun yi hira da mutane 92 waɗanda suka bamu cikakken bayanin cewar lallai an yi kisa mai yawa fiye da yadda ake zato, kuma mun yi amfani da naura mai hagen nesa ta satellite wacce ta nuna mana abubuwan da suka faru. Haka nan mutane da ke unguwanin da aka bizne mutanen sun tabbatar mana da haka''.

Sauti da bidiyo akan labarin