1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty: An azabtar da 'yan adawan Kamaru

Mouhamadou Awal Balarabe
July 26, 2019

Kungiyar Amnesty International ta bayyana cewa jami'an tsaron kasar Kamaru sun azabtar da mambobi 59 na babbar jam'iyyar adawa ta MRC, inda suke dokesu tare da tilasta musu yin tsalle kwadi.

https://p.dw.com/p/3Mnkh
Kamerun Präsidentschaftswahlen Kandidat Maurice Kamto
Hoto: Reuters/Z. Bensemra

Tun farkon watan Yuni ne aka kama 'yan hamayya da dama bayan wata zanga-zangar da suka gudanar da nufin tilasta wa gwamnatin Kamaru sakin jagoran adawa Maurice Kamto, wanda aka tsare tun daga karshen watan Janairu.  Ana tsare ne da 'yan adawan ne a wani kurkukun kare kukanka da ke ma'aikatar tsaro a Yaoundé babban birnin kasar. Dama da jumawa da kungiyoyin kare hakkin bil Adama ciki har da Amnesty Internation suke kokawa kan azabtar da wadanda ke tsare da jami'an tsaro ke yi.

Ita ma a nata bangaren jam'iyyar MRC ta yi tir da muzgana wa mataimakin shugabanta na kasa baki daya Mamadou Mota wanda aka canza wa kurkuku bayan boren da furzunoni suka gudanar a babban gidan yari Yaoundé babban birnin kasar kamaru.  A cewar daya daga cikin lauyoyinsa dai, jami'an tsaro sun ci zarafin Mamadou Mota yayin da suke sauya masa kurkuku zuwa ma'aikatar tsaro inda yake tsare yanzu haka.