Amirka:Yuwuwar daukar matakan soji a Libya | Labarai | DW | 28.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka:Yuwuwar daukar matakan soji a Libya

Kasashen Amurka da Britaniya da Faransa da Italiya na duba yiwuwar daukar matakan soji a kasar Libya a dai-dai lokacin da kungiyar IS ke cigaba da baza rassan ta a Kasar ata cewar Kasar Italiya.

Shima anasa bangaren Mai magana da yawun fadar White House ta Amirka Peter Cook yayi nuni da cewar cigaba da bazuwar 'ya'yan kungiyar IS a Libya abune mai matukar tada hankali.

Yace Amurka a shirye take wajen duba hanyyoyin da za abi don daukar matakan da suka dace don dakile a yyukan su a Libya da kasahen Iraki da Syriya.

Tun dai a shekara ta 2011 yan tawaye kasar Libya tare da goyan bayan kungiyar tsaro ta NATO suka hambarar da tsohon shugaban kasar Moamer Kadhafi daga gadon mulki to amma tun bayan hallaka shi kashe kashe da rashin tabba na zaman lafiya ke cigaba da addabar kasar.