Amirka za ta taimaka wa Iraki a kan ISIS | Labarai | DW | 20.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka za ta taimaka wa Iraki a kan ISIS

A yayin da mayakan tada-kayar-baya na ISIS ke ci-gaba da mamaye wasu yankunan kasar Iraki, Amirka da wasu kasashe sun bayyana muradinsu na bada agaji.

Shugaban Amirka Barak Obama ya ce kasarsa za ta aike da jami'an soja mashawarta fiye da dari uku don tallafa wa gwamnatin Iraki wajen magance barazanar 'yan tada-kayar-baya da suka kwace iko da yankunan kasar.

Yace" Amurka za ta ci gaba da bayar da goyon baya ga jami'an tsaron Iraki. A shirye muke wajen samar da cibiyoyin sojin hadaka a birnin Bagadaza da arewacin Iraki, domin musayar bayanan sirri, tare da shirya yadda zamu tinkari mayakan tada-kayar-baya na ISIS."

Ita ma Australiya za ta aike da karamin ayarin sojojinta, a wani mataki na abun da ta kira bunkasa matakan tsaro a harabar ofishin jakadancin kasar da ke birnin Bagadaza. Fraiminista Tony Abbott wanda ya sanar da hakan a wannan Juma'ar, ya kara da cewar matakin na da nufin tabbatar da kare lafiyar 'yan kasar ne dake Iraki.

Adai dai lokacin da mayakan fafutuka na ISIS ke ci gaba da kokarin mamaye Irakin dai, MDD ta ce a karon farko tun bayan yakin duniya na biyu, yawan 'yan gudun hijira da sukia tsere wa rigingimu ya haura miliyan 50. A rahotanta na shekara shekara hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta ce, yawan mutanen da rigingimin kasashensu ya sa su tserewa domin neman mafaka ya kai miliyan 51.2 a shekara ta 2013, lamarin kuma ya fi muni ne a kasar Siriya.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Auwal Balarabe