1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta shawo kan rikicin Kamaru

June 8, 2021

Amirka ta dauki matakin hana takadar Visa ga wadanda take zargin ke zagon kasa a rikici tsakin dakarun kasar Kamaru da 'yan awaren yankin masu magana da turancin Ingilishi.

https://p.dw.com/p/3uZ2e
USA Antony Blinken
Hoto: Alex Brandon/AP Photo/picture alliance

Yayin baiyana matakin, sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya ce kasar ta damu matuka kan yadda rikicin ke kara ta'azzara tare da yin kira ga bangarorin biyu da su hau teburin sulhu.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama a Kamaru dai sun zargi bangarorin biyu da gasa wa junansu aya a hannu, zargin da gwamnatin ta musanta ta na mai cewa, a lokuta da dama ta kama jami'an soji da laifin kisa ko cin zarafi.

Yankuna biyu na masu magana da Turancin Ingilishi dai na Kamaru ya sha fama da rikici tun a shekarar 2017, lamarin da ya haifar da asarar rayukan mutane fiye da dubu 3 yayin da wasu kimanin dubu dari 7 suka rasa matsugunnansu.