1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin Yemen na daukar sabon salo

Usman Shehu Usman
November 10, 2018

Sanarwar da ta fito daga Pentagon ta bayyana goyon bayan matakin daina tallafawa jiragen yakin Saudiyya da ke kai farmaki wadanda Amirka ce ke ba su mai da suke sha a sararin samaniya.

https://p.dw.com/p/380Tp
Saudi-Arabien Kampflugzeuge
Hoto: AFP/Getty Images/F. Nureldine

Kasar Saudiyya dai ta fara fidda sanarwar cewa a yanzu dakarunta sun kware don haka za su iya bai wa jiragensu mai a sararin samaniya, ba tare da tallafin Amirka ba. Gabanin  Saudiya ta sanar da hakan, dama can  'yan majalisar dokokin Amirka sun buka ci da Amirka ta kawo karshen wasu bangarorin da ta ke taimaka wa Saudiya musamman a yakin kasar Yemen. A yanzu haka dai Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin jama'a na duniya, suna ci gaba da yin Allah wadai da yakin kasar ta Yamen, inda miliyoyin fararen hula ke cikin bala'i sakamakon yakin na sama da shekaru hudu yanzu.