Amirka za ta dauki mataki kan Koriya ta Arewa | Labarai | DW | 29.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka za ta dauki mataki kan Koriya ta Arewa

Jakadar Amirka a MDD Nikki Haley ce ta Amirka za ta dauki wani kwakkwaran mataki na musamman kan Koriya ta Arewa biyo bayan sabon gwajin makami mai lizzami da ta yi a wannan Talata.

Amirka ta sanar da shirin daukar wani kwakkwaran mataki na musamman kan Koriya ta Arewa biyo bayan sabon gwajin makami mai lizzami da ta yi a wannan Talata da ya bi ta sarararin samaniyar kasar Japan. Jakadar Amirka a MDD Nikki Haley ce ta sanar da hakan a daidai lokacin da kwamitin sulhu na MDD  ke shirin gudanar da wani taron gaggawa a wannan Talata domin nazarin barazanar nukiliyar Koriya ta Arewa.