1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Tim Walz ya sha alwashin lallasa Trump

August 22, 2024

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Demokrat, Tim Walz ya sha alwashin cewa, shi da Kamala Harris za su lallasa abokin hammayarsu na Republican a zaben Amirka.

https://p.dw.com/p/4jlSd
Dan takarar mataimakin shugaban kasar Amirka na jam'iyyar Democrat, Tim Walz
Dan takarar mataimakin shugaban kasar Amirka na jam'iyyar Democrat, Tim WalzHoto: Charles Rex Arbogast/AP/picture alliance

Tim Walz ya sha alwashin cewa da shi da abokiyar takararsa Kamla Harris za su yi nasara kan abokin hammayarsu na jam'iyar Republican a babban zaben Amirka na watan Nuwambar 2024.

A jawabinsa a yayin babban taron jam'iyar a birnin Chicago, gwamnan jihar Minnesota, Tim Walz ya ce wannan babbar dama ce a gare shi na zama abokin takarar Kamla Harris.

Karin bayani: Zaben Amirka: Wacece Kamala Harris? 

Walz ya kuma soki manufofin jam'iyyar Republican ta Donald Trump, ya na mai cewa abun da Amirkawa ke bukata shi ne ababen da za su samar da ci gaba ga rayuwarsu. Walz ya kara da cewa, gwamnatin Trump ba za ta amfani kowa ba, face attaijirai da kuma masu tsattsaurar ra'ayi.