Amirka ta zargi Rasha da yi mata leken asiri | Labarai | DW | 12.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta zargi Rasha da yi mata leken asiri

Rahotanni daga kasar Amirka na cewa kasar Rasha ta yi amfani da na'urar kandagarkin yaki da kutsen satar bayanai ta Internet na kamfanin Kaspersky Lab wajen gudanar da leken asirin. 

Kafofin yada labaran kasar ta Amirka sun wallafa a wannan Alhamis labarin da ke cewa hukumar leken asirin kasar ta Rashar ta kwaskware wannan kandagarki na Kaspersky wanda komfutoci kimanin miliyan 400 a duniya ke aiki da shi dan kare kai daga masu kutsen satar bayanai ta intanet ta yadda ya taimaka masu wajen gano wasu bayanan sirri na tsaron kasar ta Amirka. 

Jaridar New York Time ta kasar ta Amirka ta ce hukumomin leken asiri na kasar Isra'ila ne suka yi amfani da wannan kandagarki na Kaspersky a farkon shekara ta 2014 domin satar bayanai kan tattaunawar nukiliyar da kasashen duniya ke yi da Iran, kuma a wannan lokaci ne suka gano cewa Rasha ita ma ta yi amfani da wannan fasaha wajen leken asirin Amirka.