Amirka ta yi tir da kamen masu zanga-zanga a Iran | Labarai | DW | 30.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta yi tir da kamen masu zanga-zanga a Iran

Amirka ta yi tir da Allah wadai da kamen mutanen da Iran ta aiwatar a lokacin zanga-zangar da 'yan kasar suka gudanar domin nuna rashin jin dadinsu kan tsadar rayuwa da rashin aikin yi a kasar.

A cikin wata sanarwa da kakakin fadar ma'aikatar harkokin wajen Amirkar Heather Naeurt ta fitar ta zargi mahukuntan kasar ta Iran da mayar da kasar tasu wacce ke da wadata da yin suna a tarihi a fannin raya al'adu, zuwa wata tsagerar kasa wacce ke tallar tashin hankali da zubar da jini a duniya. 

Ta kuma yi kira ga kasashen duniya da su fito fili su kawo goyon bayansu ga 'yan kasar ta Iran a cikin wannan kokowa tasu. Mutane 52 ne dai mahukuntan kasar suka kama a lokacin barkewar zanga-zangar a ranar Alhamis da kuma suka ci gaba da ita har a ranar Juma'a.