Amirka ta yaba ayyukan Faransa a Sahel
April 24, 2017Mattis ya jinjinawa kasar Faransa inda ya ce tana kasancewa a inda ya kamata ta kasance da zaran abu ya shafi yaki da ta'addanci. Sakataran tsaron na Amirka ya yi wadan nan kalamai ne yayin wani taron manema labarai a kasar ta Jibuti.
Amirka dai na goyon bayan shirin kasar Faransa na Operation Barkhane a cikin kasashe biyar na yankin Sahel da suka hada da Mauritaniya, Mali, Chadi, Nijar da kuma Burkina Faso, inda ta barwa kasar ta Faransa da ta yi wannan aiki na yaki da 'yan ta'adda a yankin na Sahel.
Amirka ta tallafa wa jiragen yakin kasar ta Faransa da mai, da kuma karfafa musayar bayannai tsakanin sojojin kasashen biyu. A kasar ta Jibuti dai Sakataran tsaron na Amirka ya gana da shugaban kasa Ismaël Omar Guelleh, da kuma babban komandan sojojin na Amirka a Afirka Janar Thomas Waldhauser.