1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta kama masu tura wa 'yan awaren Kamaru makamai

November 29, 2022

Amirka ta zargi mutanen da tattara makudan kudade da makaman da suke aike wa gida Kamaru, domin bai wa 'yan awaren da ke son kafa kasa mai suna Ambazoniya damar garkuwa da mutane da kai wa gwamnatin Kamaru hare-hare.

https://p.dw.com/p/4KFPq
Shugaban Amirka Joe Biden
Shugaban Amirka Joe BidenHoto: Susan Walsh/AP/picture alliance

Ma'aikatar shari'ar Amirka ta sanar da fara tuhumar wasu 'yan kasar uku masu tsatso da Kamaru, kan zargin tallafa wa ayyukan 'yan aware a Kamaru.

Ma'aikatar shari'a ta Amirka ta ce a ranar Litinin jami'an tsaro suka kama mutanen da ke zaune a birane dabam-dabam.

Masu shigar da kara sun ce 'yan Kamarun da tuni suka samu shaidar zama 'yan kasar Amirka sun tara kudaden da suka kai yawan dalar Amirka 350,000, inda suka aike da su ga 'yan aware domin su tayar da zaune tsaye da sunan rajin kafa kasa mai magana da Ingilishi daga cikin kasar Kamaru.