Amirka ta tsaurara matakan samar da Visa | Labarai | DW | 30.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta tsaurara matakan samar da Visa

Wannan mataki dai na zuwa ne bayan harin da aka kai a ranar 13 ga watan Nuwamba a birnin Paris, harin da 'yan bindiga dadi na mayakan IS suka dauki nauyi.

Malaysia East Asia Summit - Barack Obama

Shugaba Obama

A ranar Litinin din nan fadar White House ta Amirka ta bayyana cewa an fitar da sabbin tsare-tsare ga masu samun takardar Visa dan shiga kasarta wadanda a baya ke samu cikin sauki amma a yanzu za a matsa bincike ga matafiya daga kasashe 38 da ke shiga kasar ta Amirka ba tare da Visa ba.

Wannan mataki dai na zuwa ne bayan harin da aka kai a ranar 13 ga watan nan na Nuwamba a birnin Paris, harin da mayakan IS suka dauki nauyinsa, wani a bu da ya sake sauya tunanin Amirkawa kan batun da ya shafi tsaro.

A yanzu sashin da ke lura da harkokin tsaro na cikin gida a Amirka ya bayyana cewa za a kara neman bayanai na matafiya kan irin tafiye-tafiye da suka yi a baya, da irin kasashen da suka ziyarta, sannan a sake nazari kan bayanai na samun hotunan yatsun matafiyan da a lokutan baya ke samun takardar shiga kasar ba tare da wadannan bayanai ba. Har ila yau sashin tsaron na cikin gidan Amirka na neman karin iko na bayar da tara mai zafi ga duk kamfanin jiragen da ke kai matafiya kasar ta Amirka muddin suka yi sakaci wajen tantance takardun fasgo na matafiyan.