Amirka ta sanyawa masu tallafawa kungiyar Is kudade takunkumi. | Labarai | DW | 29.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta sanyawa masu tallafawa kungiyar Is kudade takunkumi.

Kasar Amirka ta sanyawa wasu masu tallafawa kungiyar IS da kudade takunkumi ta hanyar toshe duk wasu kafafen kudi da kungiyar ke mu'amala da su.

Baitul malin kudaden Amirkan a yayin bayar da sanarwar tace takunkumin zai fara aiki ne ga jagoror goma 15 cikin su hadda masu goya musu baya da masu gudanar da kungiyar ta ISIS.

Sanarawar ta kara da cewar mutane goma da karin wasu kungiyoyi biyar masu ayyukan ta'addanci da suka hada da 'yan kasashen Faransa da Britaniya an sanaya musu takunkumin.

Bailtul malin Amukan yace irin yadda kungiyar ke cigaba da bazuwa ya zama wajibi a dauki kwararan matakai ta hanyar dakile irin hanyoyin da suke samin tallafin kudade a gurare da dama.