1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An gano mai taimaka wa Iran da kayan kera makamai

Ramatu Garba Baba
March 30, 2022

Amirka ta lafta wa wani attajirin Iran takunkumi bayan zarginsa da siya wa gwamnatin Tehran kayayyakin kera makaman nukiliya da kasashen yammacin ke nuna damuwa a kai.

https://p.dw.com/p/49Fkg
Mohammad Jafar Montazeri
Hoto: Rouzbeh Fouladi/ZUMA Wire/picture alliance

A yayin da ake kokarin cimma yarjejeniya a tsakanin Iran da wasu manyan kasashen duniya, Amirka ta sake sanar da kakaba wa wasu manyan kamfanonin Mohammad Ali Hosseini, wani attajirin kasar ta Iran takunkumi bisa zargin hannu a sayo kayayyakin da gwamnatin Tehran ke bukata a shirin nukiliyarta.

Amirka ta ce, duk da tattaunar da ake ci gaba da yi don ganin Iran da kasashen sun cimma matsayar koma wa yarjejeniyar da aka kulla a shekarar 2015, hakan baya nufin za ta zura idanu a ci gaba da sarrafa makaman da yammacin duniya ke nuna damuwa a kansa.

A farkon wannan watan na Maris, an zargi Iran da amfani da wani nau'in makami mai linzami a Irak da kuma mara wa mayakan Houthi na Yemen baya a hare-haren da suka kai cibiyoyin man Saudiya, wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake daf da cimma yarjejeniyar da tsohon shugaban na Amirka Donald Trump ya soke a shekarar 2018.