Amirka ta kira sojoji a Burkina Faso da su mika mulki | Labarai | DW | 02.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta kira sojoji a Burkina Faso da su mika mulki

Yayin da kungiyoyi a Burkina Faso ke ci gaba da nuna adawar su ga matakin sojojin kasar na darewa kan kujerar mulki, Amirka ta yi kira da su mika mulki.

A wata sanarwa da daya daga cikin kakakin gwamnatin kasar ta Amirka Jen Psaki ta karanta ta ce kasar Amirka na Allah wadai ga yadda sojoji suke son tilastawa al'ummar kasar ra'ayoyin su na tafiyar da shugabancin rikon kwarya, sannan kuma sanarwar ta yi kira ga al'ummomin kasar ta Burkina Faso da su koma karkashin kundin tsarin mulkin kasar tare da shirya zabe na gaskiya cikin dan kankanin lokaci. Sanarwar ta Amirka ta nuna damuwarta ga mutanen da suka rasa rayukansu a wannan kasa, inda kuma ta yi kira da a kauce wa duk wani abin da zai kai ga rasa wasu rayukan nan gaba.

A wannan Lahadin 'yan adawa na kasar da ma kungiyoyin fararan hula suka hallara a wannan fili na Place de la Nation, inda daya daga cikin jagororinsu Jean-Hubert Bazié cikin wani takaitaccen jawabi na mintuna biyar ya yi kira ga masu zanga-zangar da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana ta yadda za su kare wannan nasara da suka samu ta hanyar kokuwa da sojojin kasar da ke kokarin karbe nasarar.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo