Amirka ta kashe jagoran al-Qaida a Yemen | Labarai | DW | 16.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta kashe jagoran al-Qaida a Yemen

Al-Washihi ya rasu ne a cikin wani hari da aka kai da jirgi maras matuki a maboyarsa.Tuni kungiyar tasa ta Aqpa ta maye gurbinsa da wani.

Jagoran kungiyar al-Qaida a kasar Yemen wato Al-Washihi ya halaka a cikin wani hari da wani jirgi marasa matuki wato Drohn na kasar Amirka ya kaddamar a wata maboyarsa. Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP ya ce kungiyarsa ta Aqpa ce ta tabbatar da wannan labari a cikin wani faifayen bidiyo da ta wallafa a ran Talata inda ta ce ya rasu ne tare da wasu na hannun damarsa su biyu.

Tuni kuma ta ce ta maye gurbinsa da wani mai suna Qassem al-Rimi. Ana dai kallon al-Washihi dan shekaru 37 a duniya a matsayin mutun da ke rike da matsayi na biyu a cikin kungiyar al-Qaida a duniya, kuma mutuwarsa babbar asara ce ga reshen kungiyar ta kasar Yemen.

Shi ne dai ya dauki alhakin harin ta'addancin da aka kai a kamfanin jaridar kasar Faransa ta Charlie Hebdo da ma yinkurin kai hari a wani jirgin jigilar fasinja na kasar Amirka ranar sallar Krismeti a shekara ta 2009.