Amirka ta karfafa tsaro a iyaka da Mexiko
October 30, 2018Talla
Hukumomin kula da shige da fice a kan iyakar Amirka na sa ido kan tawagar 'yan ci rani 3,500 da suka nufi gabashin kasar daga yankin tsakiyar Amirka. Shugaban Amirka Donald Trump ya jaddada shirin gwamnatinsa na gina tantunan tantance 'yan gudun hijira masu neman mafakar siyasa da ke cunkushe a kan iyakar Amirka.
Wannan na zuwa ne kasa da makonni kafin gudanar da zaben tsakiyar zango, wanda jam'iyyar Shugaba Trump na Republican ke fatan samun rinjaye a dukkannin majalisun kasar.