Amirka ta kara wa′adin dage takunkumin Sudan | Labarai | DW | 12.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta kara wa'adin dage takunkumin Sudan

Shugaban Amirka Donald Trump ya kara wa'adin watanni uku domin dage takunkumin tattalin arzikin da Amirkar ta kakaba wa kasar Sudan tun daga shekara ta 1997.

Polen Warschau Rede Donald Trump (Reuters/K. Pempel)

Shugaban Amirka Donald Trump

A ranar 13 ga watan Janairu 'yan kwanaki kafin ya bar kan karagar mulkin kasar ta Amirka, tsohon shugaban kasar Barack Obama ya dage wani bangare na takunkumin da aka kakaba wa kasar ta Sudan tsawon shekaru 20, sannan kuma ya bayar da watanni shida na sa ido ga kasar ta Sudan kafin dage ga baki dayan takunkumin da ke a matsayin wani mataki na ladabtarwa.

Amirka dai na zargin Sudan da laifin daure wa ta'addanci gindi har ma da goyon bayan jagoran kungiyar Al-Qaida Osama Bin Laden. A wannan Laraba ce dai ta kamata wa'adin watannin shida ya cika, amma kuma shugaba Trump ya sake kara wa'adin da watanni uku.