Amirka ta kara jaddada goyon bayanta ga kasar Masar | Labarai | DW | 12.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta kara jaddada goyon bayanta ga kasar Masar

Sakataren harkokin wajen Amirka Rex Tillerson ya jaddada aniyar kasarsa na ci gaba da ba kasar Masar cikakken goyon baya a kan yaki da ayyukan 'yan ta'adda.

Rex Tillerson ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da takwaransa na kasar Masar  daga nan sai ya kara da cewar Amirka ba za ta gajiya ba wajen ganin an  gudanar da zabubbuka a kasashen Larabawa bisa cancanta,kamar yadda kasar ta dauki aniyar gani ta maido da zaman lafiya tsakanin kasashen Falasdinu da Isara'la. Duk kuwa da cewar Donald Trump ya ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, a karshe ya roki al'ummar kasar Masar da su ci gaba da goyon bayan Amirka don maido da tsaro kasar.