1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta kai har kan Al Shabaab

December 30, 2019

Bayan kaddamar da wani hari mai muni da mayakan kungiyar Al-Shabaab suka yi a Somaliya, dakarun Amirka sun ce sun hallaka mayakan kungiyar.

https://p.dw.com/p/3VTtP
Afrika Senegal US Soldaten
Hoto: Getty Images/AFP/Seyllou

Rundunar sojin Amirkar da ke yankin Afirka, ta kaddamar da wasu jerin hare-hare da jiragen sama na yaki a wasu yankunan da 'yan bindigar suke a kuryar Afirka, inda ta ce ta kashe hudu daga cikinsu.

Baya ga kisan maharan a ranar Lahadi, sdakarun na Amirka sun kuma ce sun lalata wasu motocin 'yan bindigar wadanda suka amannar su ke kai hare-hare a Somaliya.

A ranar Asabar da ta gabata ne dai wata mota makare da nakiyoyi ta tarwatse a tsakiyar kasuwar Mogadishu babban birnin Somaliyar, inda akalla mutum 80 suka salwanta.

Rahotanni sun ce akwai ma wasu 'yan kasar Turkiyya biyu da ma daliban jami'a 16 daga cikin wadanda suka mutun.

Tuni ma ministan harkokin wajen Turkiyya, Mevlut Cavusoglu, ya tabbatar da mutuwar 'yan kasar tasa biyun.