1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta halaka jagoran al-Ka'ida a Yemen

Abdullahi Tanko Bala
February 7, 2020

Fadar gwamnatin Amirka White House ta sanar da kashe jagoran kungiyar al-Ka'ida a yankin Larabawa Qassem al Rimi.

https://p.dw.com/p/3XOgI
Jemen Qasim al-Raymi A-Kaida Führer getötet
Hoto: picture-alliance/dpa/Epa

Shugaban Amirka Donald Trump ya tabbatar da cewa sojojin Amirka sun halaka jagoran kungiyar jihadi ta al-Ka'ida a yankin Larabawa Qassem al Rimi.

Wata sanarwa da fadar gwamnatin Amirka White House ta fitar, ta ce Amirka ta kai farmakin yaki da ta'addanci a Yemen wanda ya yi nasarar kashe Qassem al Rimi.

Sanarwar ta ce kashe jagoran na al-Ka'ida nasara ce ga yaki da 'yan tadda kuma saura kiris a kakkabe kungiyar baki daya.