Amirka ta gargadi Siriya kan makamin guba | Labarai | DW | 17.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta gargadi Siriya kan makamin guba

Amirka ta ce za ta mayar da martani ta hanyar amfani da karfin soji muddun gwamnatin Bashar al-Assad ba ta daina yakar abokan gaba da makami mai guba a yakin Siriya ba.

Wani babban jami'in hukumar tsaron kasar Amirka Herbert Raymond Macmaster ya sanar da cewa daukar matakin ya zama dole, ganin yadda bayanai na hotuna da shedun gani da ido ke tabbatar da yadda gwamnatin Assad ke amfani da sinadarai masu guba a rikicin kasar.

Lokaci ya yi da ya kamata a dauki mataki kan gwamnatin Siriya da masu mara mata baya a mummunar akida ta yin amfani da wannan mugun makamin mai hadarin gaske inji jami'in.

A shekarar 2017 Amirka ta taba kai wani kazamin hari kan sansanin sojin gwamnatin Siriya bayan zargin cewa bangaren gwamnatin ya yi amfani da makami mai guba kan abokan gaba wanda ya halaka mutane da dama yawancinsu fararren hula.

Shugaba Assad ya sha musanta zargin yin amfani da makami mai guba a rikicin.