1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta dakatar da sayen mai daga Rasha

March 8, 2022

Shugaba Joe Biden na Amirka ya sanar da haramta shigar da mai da kuma iskar gas daga Rasha zuwa kasarsa a matsayin ladabtarwa kan mamayar da Rashar ta yiwa Ukraine.

https://p.dw.com/p/48Bre
Shugaban kasar Amirka Joe Biden
Hoto: Andrew Harnik/AP Photo/picture alliance

Dama dai Amirka da kawayenta na Turai da suka dogara da makamashi daga Rasha na shirin janye janyewa daga fannin mai na kasar da kuma harkokin tattalin arzikinta.

A shekarar da ta gabata dai Amirka ta sayo gangar danyen mai fiye da miliyan 20 daga Rasha, batun da masana ke cewa daina huldar mai da Rasha zai haifar da tashin farashinsa.

Sanata Chris Coons na Amirka na cewa, farashin makamashi zai tashi a kasar yayin da kayayyaki za su yi tsada a sauran kasashen Turai, sai dai kuma a cewarsa hakan wata hanya ce ta nuna goyon baya ga 'yancin 'yan Ukraine.