1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Covid-19: Matasa na iya allurar BioNTech

Abdullahi Tanko Bala
May 11, 2021

Allurar da Jamus ta samar na rigakafin cutar Corona ta zama ta farko da ta sami amincewa domin rigakafi ga yara 'yan shekaru 12 zuwa sama.

https://p.dw.com/p/3tECN
Symbolbild I Erste PFIZER Impfdosen erreichen Kolumbien
Hoto: Guillermo Legaria/Getty Images

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Amirka ta bada sahalewa don aiwatar da rigakafi da maganin da hadin gwiwar kamfanin BioNTech da Pfizer suka samar domin yiwa yara matasa a wani matakin cigaba na yaki da annobar corona.

A cikin wata sanarwa da mukaddashin kwamishina a hukumar abinci da magungunan ta Amirka FDA Janet Woodcock ta fitar ta ce fadada yiwa yara matasa rigakafin zai bada damar kare su daga cutar da kuma komawa rayuwa yadda aka saba tare da kawo karshen annobar baki daya.

Shugabar hukumar kula da magunguna ta tarayyar Turai Emer Cooke ta shaidawa 'yan jarida cewa sakamakon amincewa da allurar ta BioNTech ga yara 'yan shekaru 12 zuwa 15 akwai yiwuwar kungiyar tarayyar Turai za ta fara yiwa yara rigakafin a cikin wannan watan.