1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta kai karin sojoji a Bagadaza

Gazali Abdou Tasawa
December 31, 2019

Amirka ta aika da karin sojoji a Bagadaza domin bayar da kariya ga ofishin jakadancinta da ke fuskantar zanga-zanga da ma kone-kone daga magoya bayan kungiyar 'yan Shi'a ta Hezbollah a Iraki.

https://p.dw.com/p/3VXnz
Proteste bei der US-Botschaft in Baghdad
Hoto: picture-alliance/dpa/AA/M. Sudani

Amirka ta sanar da aikawa da karin sojoji a Bagadaza domin bayar da kariya ga ma'aikata da jami'an diplomasiyyarta a ofishin jakadancinta wanda ke fuskantar zanga-zanga da ma kone-kone daga magoya bayan kungiyar 'yan Shi'a ta Hezbollah a Iraki.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twiter, shugaban Donald Trump na Amirka ya zargi kasar Iran da kitsa wannan zanga-zanga ta Bagadaza tare da yi mata kashedin da ta kwana da shirin daukar alhakin duk wani abin da zai faru a ofishin jakadancin na Amirka a Bagadaza.

Dubunnan magoya bayan kungiyar 'yan Shi'a ta hezbollah a Iraki ne suka gudanar da zanga-zanga da ma kone-kone a gaban ofishin jakadancin na Amirka a birnin Bagadaza, domin nuna rashin amincewarsu da harin da sojojin Amirka suka kai wa mayakan na Hezbollah a ranar Lahadi inda suka halaka 25 daga cikinsu.