Amirka: Sabon kudirin neman tsige Shugaba Donald Trump | Siyasa | DW | 11.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Amirka: Sabon kudirin neman tsige Shugaba Donald Trump

Majalisar dokokin Amirka karkashin jagorancin jam'iyyar Demokrats ta gabatar da kudirin sake tsige Shugaba Donald Trump daga kujerar mulki, wani abin da zai  zama mummunan tabo ga Trump.

Daukar wannan mataki, ya biyo bayan zargin da ake yi wa Shugaba Donald Trump na tunzura 'yan dabar siyasarsa a ranar 6 ga watan Janerun 2021, suka kai farmaki a ginin majalisar dokoki, lokacin da wakilai suke aikin tabbatar da nasarar da Shugaba mai-jiran gado Joe Biden ya samu a zaben watan Nuwamban 2020. Ana ganin wannan abind tamkar yunkurin juyin mulki ne suka yi wa Biden, domin jaddada karerayin da Trump ya dade yana yi cewa, wai shi ya lashe zaben. Ko da yake shugaban masu rinjaye a majalisar Stenoy Hoyer ya karanta takardar kudirin, amma tun farko kakaki Nancy Pelosi ta ce;

"Ina mara wa kiran da jagoran Demokrats a majalisar dattawa ya yi ga mataimakin shugaban kasa da ya gaggauta yin amfani da sashe na 25 na kundin tsarin mulki, ya cire wannan shugaban kasa daga mulki. Idan kuma mataimakin shugaban kasa da majalisar zartarwa sun kasa yin wani abu, majalisar dokoki za ta fara aikin tsige shugaban kasa."

Kakakin majalisar wakilan Amirka Nancy Pelosi

Kakakin majalisar wakilan Amirka Nancy Pelosi

Takardar tuhumar neman tsigewar ta ci gaba da cewa Trump ya jefa yanayin tsaron Amirka da cibiyoyin gwamnati cikin mummunan hatsari. Ya yi barazana ga mutuncin tsarin dimukuradiyyar Amirka, ya tauye aikin mika mulki cikin lumana, sannan ya sabatta majalisa, wadda ita ma wani ginshiki ne na aikin gwamnati. A dangane da haka, ya saba wa amanar da aka ba shi ta shugaban kasa wanda hakan ya jikkata al'umar Amirka.

Karin bayani:Shugaba Trump na Amirka ba zai halarci rantsar da Biden ba

Ko da yake saboda kurewar lokaci, majalisar dattawa ba za ta samu sukunin yi wa Trump shari'a ba kafin ya sauka daga mulki, amma ga alama, ko a cikin jam'iyyar tasa ta Republican, akwai wakilai da kuma sanatoci irinsu Lisa Murkoski da Pat Toomey da a wannan karon suka juya wa Trump baya. Ga ma abin da Toomey ke cewa:

"Shugaban ya aikata laifukan da ya kamata a tsige shi daga mulki, amma ban san yadda za ta kaya ba a majalisar dattawa."

Magoya bayan Shugaba Trump lokacin da suka kai farmaki a cikin ginin majalisar dokokin Amirka

Magoya bayan Shugaba Trump lokacin da suka kai farmaki a cikin ginin majalisar dokokin Amirka

Nan da zuwa ranar 14 ga watan nan na Janeru, ake kyautata zaton babban zauren majalisar dokokin mai wakilai 435 zai ka da kuri'ar tsige Trump. Ayar tambaya ita ce, shin ko wannan mataki na kokarin sake tsige Trump, zai haifa wa Amirka abin kirki? Anya kuwa ba zai kara dugunzuma siyasar kasar ce ba, duba da miliyoyin magoya baya da Trump yake da su? A dai-dai wannan lokaci da ake ci gaba da zaman dar-dar, ba a san yadda ranar rantsar da Biden za ta kasance ba.

Sauti da bidiyo akan labarin