Amirka: Sabon babin dangantaka da Turkiyya | Labarai | DW | 28.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka: Sabon babin dangantaka da Turkiyya

Amirka ta sanar a wannan Alhamis cewa za ta sake bude ofishin huldar jakadancinta da ke Ankara babban birnin kasar Turkiyya bisa abin da ta kira wanzuwar zaman lafiya da ingantar tsaro da aka samu a kasar.

Matakin na nufin kasashen biyu za su ci gaba da yin hulda kamar yadda suka saba a baya dama bayar da takardar izinin shiga kasashen juna a kasar da ta sha fama da ayyukan kungiyar IS da kuma rikicin cikin gida da ya biyo bayan yunkurin juyin mulki. An sami sa-in-sa da ya kai ga tsamin dangantaka bayan da hukumomin Turkiyyan suka kama tare da tsare wani jami'in a ofishin jakadancin kasar Amirka a watan Oktoba. Tuni dai Turkiyya ta baiyana farin ciki kan sanarwar Amirka.