Amirka na kalubalantar Koriya ta Arewa | Labarai | DW | 28.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka na kalubalantar Koriya ta Arewa

Amirka ta ce za ta iya tattaunawa da Koriya ta Arewa a kan shirin ta na Nukiliya kamar yadda sakataran harkokin wajen kasar Rex Tillerson ya bayyana.

Rex Tillerson ya bayyana haka ne gabannin wata tattaunawa da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya  ya  gudanar a kan Koriya ta Arewa. Gwamnatin  Donald Trump wacce tun farko ta dage a kan matsayin yin amfani da karfin soji a kan Koriya ta Arewa, a yanzu ta sassauto, domin bin hanyoyin diplomasiya don warware takaddamar.