Amirka na fatan zaman lafiya a Sudan | Labarai | DW | 30.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka na fatan zaman lafiya a Sudan

Hukumomin Amirka da Sudan sun tattauna a Khartoum babban birnin kasar na neman mafita don kawo karshen rikicin Darfur.

Der US-Sondergesandte Donald Booth im September 2013

Jakadan Amirka a Sudan Donald Booth

Jakadan Amirka a kasashen Sudan da Sudan ta kudu Doanld Booth ya gana da wani babban na hannun daman shugaban Sudan a birnin Khartoum domin tattauna kawo karshen rikicin yankin Darfur bayan da tattaunawar tsagaita wuta ta ci tura.

Bayan kammala ganawa da jami'in Sudan Ibrahim Mahmoud, jakadan na Amirka Donald Booth ya shaidawa manema labarai cewa kawo karshen rikicin Darfur muhimmin mataki ne na samar da dorewar zaman lafiya, yace:

"Mun tattauna hanyoyin da za'a ci gaba domin kawo zaman lafiya, na kuma baiyana sha'awar da Amirka ke da ita na ganin zaman lafiya ya tabbata a Sudan kuma mun yi imani tsagaita wuta babban mataki ne a dangane da haka."