Amirka na bukatar a tsagaita wuta a Siriya | Labarai | DW | 12.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka na bukatar a tsagaita wuta a Siriya

Amirka ta gabatar da wani daftarin kudiri a gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na nema a tsagaita barin wuta.

USA UN Sicherheitsrat Nikki Haley (picture-alliance/newscom/J. Angelillo)

Nikki Haley jakadiyar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya

Jakadiyar Amirka a Majajalisar ta Dinkin Duniyar Nikki Haley wace ta bayyana kudirin ta soki lamirin Rasha da Siriya da gaza aiwatar da yarjeniyar dakatar da bude wutan da aka cimma a makonin da suka gabata. Babban magatagarda na MDD Antonio Guterres ya ce akwai bukatar gaggawa ta isar da kayan agaji na jin kai a gabashin Ghouta.